Shugaban kamfanin jiragen United Airlines Limited, Farfesa Obiora Okonkwo, ya ce duk da koke-koken fasinjoji kan tsadar tikitin jirgi, zirga-zirgar jiragen cikin gida a Nijeriya na daga cikin mafi arha a duniya.
Okonkwo, wanda shi ne kakakin kamfanonin jiragen sama a Nijeriya, ya bayyana haka ne a shirin Morning Brief na Channels TV, inda ya ce kamfanonin jirgi na aiki ne a karkashin matsin tattalin arziki mai tsanani, amma har yanzu suna kokarin rike farashi a kasa idan aka kwatanta da sauran kasashe.
A cewarsa, kamfanonin jirage a duniya na amfani da jirage iri daya kuma suna biyan ma’aikata kusan iri daya, na Nijeriya na fuskantar manyan kudade kamar haraji da yawa, bashi mai tsananin ruwa, da kuma kashe-kashen da ake biya da dalar Amurka.
Ya karyata zargin cewa kamfanonin jirgi na yin tsauraran farashi da gangan, yana mai cewa karin kudin tikiti da ake gani a yanzu ya samo asali ne daga karuwar bukatar tafiya a lokacin bukukuwan karshen shekara, kamar yadda ake gani a sauran kasashen duniya.



