Babbar Kotun Abuja da ke Gwarinpa, ta amince tsohon Ministan Kwadago, Chris Ngige, ya cigaba da cin gajiyar belin da hukumar EFCC ta ba shi tun da farko.
Alkaliyar kotun, Mai shari’a Maryam Hassan, ta bayar da wannan hukunci ne yayin yanke shawara kan bukatar beli da lauyan Ngige, Barista Patrick Ikwueto (SAN), ya shigar a madadinsa.
Kotun ta umarci Ngige da ya gabatar da mai tsaya masa wanda dole ne ya kasance darakta a aikin Gwamnatin Tarayya kuma mai fili. Haka kuma, kotun ta ce dole ne mai tsayawar ya ajiye takardun filin da kuma takardun tafiyarsa a gaban kotu har sai Ngige ya karbo fasfonsa na kasa da kasa.
Tun da farko, EFCC ta ba Ngige beli ne bisa amincewar kansa, inda ta umarce shi da ya mika takardun tafiyarsa tare da gabatar da mai tsaya masa guda daya.



