’Yan bindiga sun kai hari kauyen Fananawa da ke karamar hukumar Bukuyum ta jihar Zamfara, inda suka halaka mutum ɗaya tare da sace mutane biyar, a daren Asabar.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ’yan bindigar sun kutsa cikin ƙauyen tun cikin dare har zuwa wayewar gari.
Wani mazaunin ƙauyen, Malam Sani, ya bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen da dare, inda suka halaka mutum ɗaya, suka sace mutane, sannan suka harbe wani mutum da ya samu mummunan rauni, wanda aka kai shi Asibitin koyarwa na Sokoto domin jinya.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro suna kokari domin kubutar da wadanda aka sace kuma nan ba da jimawa ba za a ji labari mai daɗi.



