Daga: Farfesa Usman Yusuf
Litinin : 22 Disamba 2025
Ban taɓa gudu ko ja da baya ba ko nuna wata fargaba wajen bayyana matsayina a kan yaƙin da ake kan yi da ‘yan fashin daji da aka kwashe shekara goma sha biyu ke nan ana ta fama.
Wannan ‘yancina ne na faɗin albarkacin bakina a matsayina na ɗan ƙasa da lamarin ya shafe ni kai tsaye nake cikinsa tsundum ba wai mai rungume hannu ya zura ido kawai ko wanda ya ƙware wajen haddasa fitina ba.
Na yi wannan ɗan rubutu ne domin jaddada matsayin da na kwashe fiye da shekara 6 ina nanatawa a cikin rubuce-rubucena masu yawan gaske da hirarrakin da aka yi da ni a gidajen rediyo da talabijin daban-daban.
Mun san cewa waɗannan fitintinu na ‘yan fashin daji sun somo ne a matsayin matsaloli na zamantakewa da wasu dalilai na cikin gida suka haifar, sanadiyyar halayyar wasu ‘yan siyasa da ba su san ciwon kan su ba, suka yi sake suka yi watsi da lamarin har ƙaramar magana ta zama babba, har take nema a yanzu haka ta jefa duka ƙasar cikin mawuyacin hali.
A shekarun nan goma sha biyu, martanin da gwamnatocin jihohi da na tarayya suke mayarwa shi ne na ci gaba da cusa soja cikin wannan taƙaddama da mummunan sakamako.
Akwai lokacin da yake takamaiman aikin da ya kamata a ce na soja ne, amma ba ta amfani da ƙarfin soja ba ne za a iya shawo kan wannan matsala ta ‘yan fashin daji. Saboda a tarihi na taƙaddama, ko faɗace-faɗace irin wannan, ba a taɓa samun nasara a fagen daga ba.
Na sha faɗi ina nanatawa cewa duka matsalolin, matsaloli ne na cikin gida kuma dole ne maganinsu yana nan a cikin gida ba sai an je da nisa ba.
Wasu manyan tsare-tsare daga Abuja ba tare da an sanya masu ruwa da tsaki na cikin gida ba, ba su taɓa haifar da ɗa mai ido ba tsawon shekaru 12 da suka wuce, kuma ba za su taɓa yin wani tasiri ba.
Saboda haka, ci gaba da maimaita abu guda a yi tsammanin za a samu wani sakamako daban tamkar ana iya cewa mafarki ake yi.
Gaskiyar maganar shine, aikin ya yi wa sojojinmu yawa don ana ta tuttura su duka jihohi 36 na ƙasar nan har da Babban Birnin Tarayya Abuja. Sojoji na ci gaba da gajiya da jigata saboda daukar tsawon lokaci suna kai-komo har wasun su suna fita hayyacin su, wasu kuma su koma suna mu’amala da miyagun ƙwayoyi.
Dole ne mu saurari koke-koken neman taimako daga ‘ya’yanmu wanda sune mayaƙanmu da suke sadaukar da rayuwarsu a kowacce wayewar garin Allah saboda mu.
Babu yadda za a iya samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan al’ummar da ke da tsananin rashawa irin na Nijeriya, ga rashin shugabanci na gari, ga yunwa da gwamnati ta ƙaƙaba wa jama’a, ga matsananciyar fatara, ga yara ba sa zuwa makaranta, ga matasa ba aikin yi, ga mu’amala da miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa, ga ƙaruwar gilmawar ƙananan makamai, ga gubar ƙiyayya da rashin yarda tsakanin mabiya addinai daban-daban, da ƙabilanci da ya yi katutu da kuma jin haushin juna da ‘yan siyasa da ba su san ciwon kan su ba, suke ci gaba da rurutawa.
Zuba jari ba ɗan kaɗan ba ga shawo kan waɗannan matsaloli na zamantakewa zai fi taimakawa wajen rage kashe kuɗaɗe da ceto rayuwa maimakon ci gaba da zubar da jini da ci gaba da kashe maƙudan kuɗi ɓangaren soja.
Rashin sa Sarakunan Gargajiya, da Malamai, da Dattawa da shugabannin al’umma cikin neman maslahar wannan matsalar tun da farko, babban kuskure ne da ke buƙatar a yi gyara a kan sa.
Tattaunawa ta sulhu da sasanci halastacciyar hanya ce ta warware dukkan wani rikici, da ya kamata a bi ta ɗoɗar domin kai wa ga dauwamammen zama lafiya.
Za a iya kwance ɗamara da karɓe makaman ‘yan fashin daji, da ‘yan bijilante da dukkan sauran ‘yan ta’adda da ke riƙe da makamai ne, bayan tattaunawa da sulhu na tsakani da Allah, da ke iya maido da yarda da amana da tsohuwar ‘yan uwantaka da shekaru da aka kwashe ana zubar da jinin juna babu gaira babu dalili suka ɗaiɗaita.
A daidai lokacin da wannan yaƙin ke shiga shekararta ta goma sha uku a shekarar da ke shirin kankama ta 2026, ya kamata Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan ƙasar nan ya faɗaɗa tintiɓa tare da ba da umarnin a canza tako wato a canza salon yadda ake wannan yaƙi da ta’addamci.
‘Yan Nijeriya sun gaji da wannan yaƙi da zubar da jini da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
Usman Yusuf, Farfesa ne Ɓangaren Cututtukan Da Suka Shafi Jini da kuma Dashen Ɓargo.



