Jam’iyyar APC ta ce Shugaba Bola Tinubu ya nuna jarumtaka ta musamman da jajircewa wajen tafiyar da Nijeriya cikin sauye-sauyen tattalin arziki da na gwamnati masu wahala amma suka zama dole a shekarar 2025.
A cikin rahoton ƙarshe na shekara kan halin ƙasa, wanda Seye Oladejo, Sakataren Yada Labarai na APC na Jihar Legas ya sanya hannu, jam’iyyar ta ce 2025 ta kasance lokacin da ake buƙatar shugabanci mai ƙarfin hali da yanke shawara mai wuya.
Jam’iyyar ta yi suka ga wasu ’yan siyasa da suka yi amfani da wahalhalun sauye-sauyen don nuna Nijeriya a matsayin ƙasa mai gazawa domin cin moriyar siyasa, inda ta ce wannan adawa babu kishin ƙasa sai dai manufar cutar da ƙasa.



