Hukumar kula da gidajen ajiya da gyaran hali ta Nijeriya ta bayyana cewa akalla daurarru 27,416 ne aka yanke wa hukunci a fadin kasar cikin shekarar 2025.
Ta kuma ce a halin yanzu akwai mutane 50,703 da ke jiran shari’a a daidai lokacin da ake bankwana da 2025.
Wannan dai na cikin wani sabon rahoto da hukumar ta fitar, wanda ke nuna irin kalubalen cinkoso da ake samu a gidajen yarin da ke fadin kasar, kamar yadda jaridar Punch ta wallafa.
A hannu guda, hukumar ta NCoS ta nuna damuwa da cewa yawan wadanda ke zaman jiran shari’ar na kasancewa wani nauyi ga gwamnati, musamman ta bangaren kudaden da ake kashewa wajen kula da su.



