Kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami SAN tare da ɗansa da ɗaya daga cikin matansa a gidan gyaran hali na Kuje.
Mai shari’a Justice Emeka Nwite ne ya bayar da umarnin a ranar Talata, 30 ga Disamba 2025, bayan sauraron hujjoji daga lauyoyin wadanda ake tuhuma karkashin jagorancin Joseph Daudu SAN da kuma lauyan masu gabatar da ƙara na EFCC Ekele Iheneacho SAN.
Malami, tare da ɗansa Abubakar Malami da matarsa Asabe Bashir na fuskantar tuhumar badakalar kuɗi guda 16, wadda hukumar EFCC ta shigar a kansu.
EFCC na zargin cewa wadanda ake tuhumar sun haɗa kai a lokuta daban-daban wajen canza salo na kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya, waɗanda darajarsu ta kai Naira biliyan 8.7.



