DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Bankunan Nijeriya za su fara cire harajin N50 daga masu tura kudi ta banki da suka kai N10,000

-

Daga 1 ga watan Janairun, 2026, bankunan Nijeriya za su fara cire harajin N50 kan duk wanda ya tura kudi da ya kai ₦10,000 ko sama da haka, bisa tanadin sabuwar dokar haraji (Tax Act) da aka kafa.

Jaridar Punch ta rawaito cewa bankunan kasuwanci irinsu UBA da Access Bank, ne suka fara sanar da kwastomominsu game da aiwatar da dokar kafin fara aiki da ita.

Google search engine

A cewar UBA, sabon tsarin ya canza daga yadda ake yi a baya, inda za a rika cire N50 sau ɗaya kacal kan kowane harkar tura kudi da ta kai adadin da aka kayyade.

Bankin ya ƙara da cewa wanda ya tura kuɗi ƙasa da N10,000 ba za a caje su ba, haka kuma masu albashi an keɓance su daga harajin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

KasashenNijar, Burkina Faso da Mali sun sanar da kakaba wa ’yan Amurka takunkumin biza

Kasashen Nijar,Burkina Faso da Mali sun sanar da kakaba takunkumin biza ga ’yan ƙasar Amurka, a matsayin martani ga dokar hana shige da fice da...

Sojoji sun ceto mutane 1,023, tare da kwato bindigogi 189 Arewa maso Yammacin Nijeriya

Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewa ta ceto mutane 1,023 da aka sace, tare da kwato bindigogi AK-47 guda 189 da alburusai 4,338, a sumame...

Mafi Shahara