Tsohon gwarzon damben duniya Anthony Joshua ya koma Birtaniya bayan hatsarin mota a Najeriya da ya yi sanadin mutuwar Latif Ayodele da Sina Ghami.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa ‘Yan sanda sun gurfanar da direban motar, Adeniyi Mobolaji Kayode, kan tuhumar tukin ganganci da ya haddasa rasa rai, inda zai gurfana a kotu ranar 20 ga Janairu.
Hatsarin ya faru ne a hanyar Lagos–Ibadan bayan motar da suke ciki ta buge wata mota da aka aje a gefen hanyar.
Joshua ya samu raunika kaɗan kuma an sallame shi daga asibiti, kuma ya koma Birtaniya ne gabanin jana’izar abokan aikinsa.



