DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ramaphosa ya yi Allah-wadai da kama Maduro da Amurka ta yi

-

Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta ɗauka na kama Shugaban ƙasar Venezuela, Nicolas Maduro.

Ramaphosa ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, inda ya ce Afirka ta Kudu na tare da al’ummar Venezuela kan abin da ya faru.

Google search engine

Ramaphosa ya kuma yi kira ga kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya UNSC da ya ɗauki mataki cikin gaggawa domin cika aikinsa na samar da zaman lafiya da tsaro a duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dangote ya janye korafin zarge-zargen cin hanci da ya shigar a hukumar ICPC kan Farouk Ahmed

Dangote ya janye korafin zarge-zargen cin hanci da ya shigar a hukumar ICPC kan Farouk Ahmed, tsohon shugaban hukumar NMMPRA Jaridar Daily Trust ta ce attajirin...

Nijeriya na bin kasashen Nijar, Togo da Benin tulin bashin kudin lantarkin da ya kai N25bn – NERC

Hukumar kula da lantarki ta Nijeriya NERC ta ce, kasar na bin kasashen Togo, Nijar da Benin bashin dala $17.8m — kimanin N25bn na lantarkin...

Mafi Shahara