DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Nijeriya na biyan tallafin lantarki kusan tiriliyan 2 a duk shekara

-

Rahotannin Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) sun nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta kashe naira tiriliyan 1.98 a matsayin tallafin wutar lantarki cikin watanni 12, daga Oktoba 2024 zuwa Satumba 2025.

A cewar rahoton, an kashe Naira biliyan 471.69 a zangon karshe na 2024, Naira biliyan 536.4 a zangon farko na 2025, Naira biliyan 514.35 a zangon na biyu, sannan Naira biliyan 458.75 a zango na uku na 2025 kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Google search engine

NERC ta bayyana cewa wannan tallafi na biyo bayan kasancewar kudin wutar lantarki a kasa da kudin da ake kashewa wajen samar da ita, wanda ya tilasta wa gwamnati rufe gibin ta hanyar tallafi. Rahoton ya ce ana aiwatar da tallafin ne kai tsaye ta hanyar rage kudin da kamfanonin rarraba wuta ke biya wa Hukumar Sayen Wuta ta Kasa (NBET).

Duk da karin kudin wuta ga masu amfani da Band A tun Afrilun 2024, nauyin tallafin bai ragu ba. Hakan ya sa Ministan Wuta, Adebayo Adelabu, da masana ke jaddada cewa tsarin tallafin wuta ba mai dorewa ba ne, tare da kiran a mayar da tallafin ne ga talakawa kadai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaba Trump ya yi sabuwar barazanar kara kawo sabbin hare-hare a Nijeriya

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake yin barazanar sake kai hare-haren a Nijeriya idan aka ci gaba da kashe Kiristoci, duk da musanta wa da...

‘Yan Nijeriya 408,000 ne ke gudun hijra a Nijar, Kamaru da Chadi ta dalilin matsalolin tsaro in ji MDD

Fiye da ‘yan Nijeriya 408,000 ne ke ci gaba da gudun hijira a kasashen Nijar, Kamaru da Chadi, sakamakon matsalar rashin tsaro da ya addabi...

Mafi Shahara