Fiye da ‘yan Nijeriya 408,000 ne ke ci gaba da gudun hijira a kasashen Nijar, Kamaru da Chadi, sakamakon matsalar rashin tsaro da ya addabi yankin Arewa maso Gabashin ƙasar tun shekarar 2009, a cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNHCR.
Rahoton UNHCR na shekarar 2025 ya bayyana cewa Jamhuriyar Nijar ce ke dauke da mafi yawan ‘yan Nijeriya da ke gudun hijira a can, inda ake da mutane 258,653, yawancinsu na zaune a yankin Diffa, kusa da kananan hukumomi kamar Kuluk, Gashua, Machina da Malkotan.
Kasashen Kamaru na dauke da ‘yan gudun hijira 126,892, mafi yawansu na sansanin Minawao da ke yankin Far North, yayin da Chadi ke dauke da mutane 21,636, musamman a yankin Lac Province da Baga Sola.



