Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta ce ta dakile yunkurin harin ’yan bindiga a kauyen Guda Lamido, da ke garin Kashere a karamar hukumar Akko kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:00 na safiyar Talata, 13 ga Janairu, inda aka samu rahoton cewa wasu ’yan bindiga sun yi yunkurin kutsawa cikin kauyen.
Ya ce jami’an ’yan sanda tare da ’yan banga da mafarauta sun gaggauta kai dauki, inda suka fafata da ’yan bindigar tare da tilasta musu guduwa zuwa daji.
DSP Abdullahi ya ce babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata, kuma an dawo da zaman lafiya a yankin. Ya kara da cewa an tsaurara sintiri da sa ido domin hana sake aukuwar barazana, tare da yin kira ga jama’a da su cigaba da bai wa hukumomin tsaro hadin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai kan duk wani motsi na barazana.



