Jam’iyyar APC ta musanta rahotannin da ke cewa ana shirin sauya Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a matsayin abokin takarar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a zaɓen 2027.
Sakataren Yaɗa Labarai na APC na Ƙasa, Felix Morka, ne ya yi wannan bayani a shirin Politics Today na Channels a ranar Litinin, inda ya ce rade-radin ba su da tushe.
“Yin hasashe kan sunayen mutanen da za su maye gurbin Mataimakin Shugaban Ƙasa kuskure ne. Bisa Dokar Zaɓe da dokokin ƙasa, an hana duk wasu harkokin kamfe yanzu. Bai kamata mu riƙa tattauna wannan batu sosai ba, yadda kafafen watsa labarai da jama’a ke yi.” In ji shi.



