Mai shari’a Emmanuel Subilim na kotun ma’aikata ta Nijeriya ya bai wa daukacin ma’aikatan Abuja da ke yajin aiki umarnin su dakatar har zuwa lokacin da za a sake zaman sauraron shari’ar.
Wannan umarni ya biyo bayan karar da ministan Abuja Nyesom Wike ya shigar gaban kotun, yana neman ta tilasta wa ma’aikatan komawa bakin aiki.
A cewar mai shari’ar, wajibi ne a dakatar da duk wani sabani aka mika shi gaban kotu, har sai ta kammala aikinta, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya wallafa.
Kazalika ya ce duk wanda aka samu da kin bin umarni ko sabawa doka tabbas zai fuskanci hukunci.



