Rumbun wutar lantarki na Nijeriya ya sake faduwa a karo na biyu cikin wannan shekarar ta 2026 a ranar Talata.
Kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, bayanai sun nuna cewa a lokacin haɗa rahoton, babu ko megawatt ɗaya da ake samarwa ga kamfanonin rarraba wuta 11 na ƙasar.
Wannan na zuwa ne bayan da grid ɗin ya fuskanci faduwa karo na farko a bana a ranar Juma’a da ta gabata, wanda kuma ya zo makonni kaɗan bayan irin wannan matsala a ranar 29 ga Disamba, 2025.
Har zuwa lokacin da aka kammala rahoton, Hukumar Rarraba Wutar Lantarki ta Nijeriya (TCN) ba ta fitar da cikakken bayani kan abin da ya jawo wannan matsala ba.



