Gwamnatin China ta sha alwashin tallafa wa kasar Cuba bayan da Amurka ta yi mata barazana.
Gwamnatin Trump dai ta umarci Cuba da ta dauki matakin kulla yarjejeniya da ita, ko kuma ta fuskanci irin halin da Venezuela ta tsinci kanta a ciki.
A kwanakin baya sojojin Amurka sun kutsa cikin birnin Caracas tare da yin awon gaba da shugaban Venezuela Nicolas Maduro.
Sai dai mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China Guo Jiakun ya yi tir da lamarin, tare da bayyana cikakken goyon baya ga Cuba, kamar yadda ta saba yi a baya.



