Ma’aikatan Abuja sun jaddada cewa za su ci gaba da yajin aiki, duk da umarnin kotu da kuma barazanar takunkumi daga Ministan Abuja Nyesom Wike.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa yajin aikin, wanda kungiyoyin ma’aikata na hadin gwiwa ke jagoranta, ya fara ne a ranar Litinin bisa gazawa wajen magance korafe-korafe, da kuma tauye hakkin ma’aikata.
Daga cikin bukatu 14, ma’aikatan na neman biyan alawus na watanni biyar,sakamakon yajin aikin ya dakatar da ayyuka a Sakatariyar Abuja da wasu hukumomi da dama, ciki har da makarantun firamare da sakandare a kananan hukumomi shida.



