DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An kama ɗan jaridar Mali bisa zargin cin mutuncin shugaban Nijar, Janar Tiani

-

Hukumomin ƙasar Mali sun kama tare da tsare ɗan jarida Youssouf Sissoko, bisa zargin cin mutuncin shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar, Janar Abdourahamane Tiani.

Sissoko, wanda shi ne Daraktan Jaridar Alternance a Mali, an kama shi ne a ranar Alhamis, 5 ga Fabrairu 2026, bayan jaridar tasa ta wallafa wani labari da a ciki ta caccaki Janar Tiani, tare da zarginsa da ɗora alhakin harin da ƙungiyar IS ta kai a Yamai kan Faransa, Bénin da Côte d’Ivoire.

A cikin labarin, jaridar ta kuma zargi Janar Tiani da ƙarya, tare da cewa yana ƙoƙarin mayar da ƙasar Nijar wani dakin gwaje-gwaje na siyasar guba.

Sai dai ƙungiyar ’yan jarida masu zaman kansu ta riga ta bayyana damuwarta kan kamun Sissoko, inda ta bukaci a bayar da belinsa kafin ranar 9 ga Maris 2026, ranar da ake sa ran a gurfanar da shi gaban kotu.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dan majalisar wakilan Nijeriya ya sauys sheka daga PDP zuwa ADC

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tambuwal/Kebbe a jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, inda ya koma ADC. A cikin wasiƙar...

Sanata Wamako ya raba wa marayu su 10,000 tallafin N1,000 kowane a jihar Sokoto

Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta Arewa, Aliyu Magatakarda Wamakko, ya bayar da tallafin miliyan 10, ga mutane dubu 10 da...

Mafi Shahara