Hukumar Rajistar Kamfanoni ta Nijeriya (CAC) ta bayyana cewa ta soke rajistar kamfanoni sama da 400,000 da ba sa aiki daga kundin rajistar kamfanoni a shekarar 2025, a matsayin wani bangare na sauye-sauyen da ake yi domin inganta gaskiya, kare tattalin arziki, da dawo da amincewar masu zuba jari.
Babban Darakta na CAC, Hussaini Magaji, SAN, ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Abuja yayin tattakin motsa jiki na wata-wata da hukumar ta shirya, cikin ayyukan bikin cikar CAC shekaru 35 da kafuwa.
Magaji ya ce yawancin kamfanonin da abin ya shafa sun dade ba sa mika rahotannin shekara-shekara na doka, kuma ba sa gudanar da wani aiki, yana mai gargadi cewa irin wadannan kamfanoni na iya jefa tattalin arziki cikin hadari.


