DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Akpabio ya caccaki masu sukar aikin gyaran Dokar Zaɓe da majalisar dattawa ke yi

-

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya kare matakin Majalisar kan gyaran Dokar Zaɓe, yana mai cewa masu sukar aikin na yanke hukunci ne tun kafin kammala bin tsarin dokar.

Akpabio ya jaddada cewa Majalisar ba ta cire tsarin aika sakamakon zaɓe ta na’ura daga dokar ba, sai dai ta ɗora ayar tambaya kan sharadin aika sakamakon a lokacin da ake yin zaɓe.

A cewar wata sanarwa da jaridar Punch ta ruwaito, Akpabio ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin da ya halarci bikin kaddamar da littafin The Burden of Legislators in Nigeria na Sanata Effiong Bob, inda ya kasance bako na musamman.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dan majalisar wakilan Nijeriya ya sauys sheka daga PDP zuwa ADC

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tambuwal/Kebbe a jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, inda ya koma ADC. A cikin wasiƙar...

Sanata Wamako ya raba wa marayu su 10,000 tallafin N1,000 kowane a jihar Sokoto

Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta Arewa, Aliyu Magatakarda Wamakko, ya bayar da tallafin miliyan 10, ga mutane dubu 10 da...

Mafi Shahara