Madugun adawa a Nijeriya Atiku Abubakar, ya buƙaci Gwamnatin kasar da ta ta bayyana dalilin tsare tsohon Kaduna, Nasir El-Rufai, bisa rahotannin da ke nuna cewa lafiyarsa na fuskantar barazana, tare hana iyalansa da lauyoyinsa damar ganinsa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Atiku ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa ga iyalai, abokai da masu goyon bayan El-Rufai, yana mai cewa Gwamnatin Nijeriya na da alhakin bayyana dalilin da yasa hukuma ke tsare shi.
Atiku ya ce hakan na ƙara haifar da shakku a zukatan jama’a, tare da jaddada cewa kundin tsarin mulki ya tanadi kare mutunci, lafiyar wanda ake tsare da shi, da ba shi damar samun kulawar lafiya.



