Ma’aikatar harkokin tsaron cikin gida ta jihar Katsina ta bayyana cewa rundunar rundunar sojin Nijeriya ta yi ajalin ‘yan bindiga 45 a wani artabu da ya faru a karamar hukumar Danmusa.
A wata sanarwar da kwamishinan ma’aikatar, Nasir Mu’azu, ya fitar ta ce an gudanar da wannan farmaki ne bayan samun bayanan sirri daga jami’an tsaro.
Daga cikin ‘yan bindigar da aka halaka akwai Alti, wanda ake cewa shi ne ɗan uwan shahararren jagoran ‘yan bindiga Adamu Alieru, haka kuma an kashe wani fitaccen dan bindiga da ake kira Damale.



