Paparoma Leo XIV ya yi addu’a a ranar Lahadi cewa ƙarar fashe-fashe da ake samu a Gabas ta Tsakiya za ta dakata, yayin da rikicin da ya biyo bayan hare-haren sama na Amurka da Isra’ila a Iran ke shiga rana ta tara.
Ya nuna damuwarsa kan yaduwar tashin hankali da tsoron cewa wasu ƙasashe, ciki har da Lebanon, na iya fada wa cikin rashin tsaro.
A baya ma, gidan talabijin na Channels ya ambato shugaban darikar Katolikan ta Duniya na kira ga shugabannin kasashen da abun ya shafa su daidaita tsakaninsu ta hanyar sulhu.



