DCL Hausa Radio
Kaitsaye

MDD ta magantu kan harin bam a Gwoza jihar Borno

-

Ko’odinetan Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya, Mohamed Malick Fall, ya fitar da wata sanarwa inda ya yi kakkausar suka kan harin kunar bakin wake da aka kai kan fararen hula a Karamar Hukumar Gwoza da ke Jihar Borno.
Hare-haren da suka auku a ranar Asabar, 29 ga watan Yuni, sun yi sanadin asarar rayuka da har yanzu ba a san adadinsu ba, inda rahotanni ke nuni da cewa an kashe mutane da dama tare da jikkata wasu da dama.
“Majalisar Dinkin Duniya ta yi kakkausar suka kan harin kunar bakin wake da aka kai kan fararen hula a karamar hukumar Gwoza da ke jihar Borno. Har yanzu dai ba a san adadin mutanen da aka kashe da kuma jikkata ba, amma bisa ga dukkan alamu an kashe mutane da dama da kuma munanan raunuka”.
Da yake bayyana firgicinsa kan yadda ake kai wa farar hula hari, Mista Fall ya yi Allah wadai da wadannan ayyuka da kakkausan harshe tare da nuna goyon baya ga gwamnatin Najeriya da iyalai da al’ummomin da abin ya shafa.
“Na firgita da wannan harin da aka kai wa farar hula, kuma na yi Allah wadai da irin wadannan ayyuka da kakkausan harshe. Ina goyon bayan gwamnatin Najeriya da iyalai da al’ummomin duk wadanda abin ya shafa.
“A madadin Majalisar Dinkin Duniya, ina tunatar da dukkan bangarorin da ke rikici da su kiyaye hakkinsu a karkashin dokokin jin kai na kasa da kasa na kare fararen hula daga cutarwa”, in ji shi.
Bugu da kari, Mista Fall ya mika ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Borno tare da bayar da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji don taimakawa wadanda harin ya rutsa da su.
“Na tuntubi Gwamnatin Jihar Borno domin in jajanta mata tare da bayar da duk wani tallafi da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji za su iya bayarwa don taimakawa wadanda harin ya rutsa da su.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Yan kasuwar mai sun sauke farashin man fetur kasa da yadda Dagote ke sayarwa

Wasu masu shigo da man fetur daga ƙasashen waje sun fara sayar da shi a ƙasa da Naira 860 kowace lita, lamarin da ya sauka...

Saurayi ya gaggabe wa budurwarsa hakora shida a Legas

Wani saurayi a unguwar Ibadan dake Ebute Meta, jihar Legas, ya lakadawa budurwarsa Fatima, wadda ke sana’ar gyaran kai, dukan da ya janyo ta rasa...

Mafi Shahara