Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya dage cewa hadin gwiwa tsakanin jam’iyyu ita ce kawai hanyar da za su iya kayar da shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.
Atiku ya nuna adawa da matsayin gwamnonin jam’iyyar PDP wadanda suka nisanta jam’iyyar daga kawancen da tsohon mataimakin shugaban kasar ke shirin yi.
A ranar Litinin, kungiyar gwamnonin PDP karkashin jagorancin gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, sun bayyana cewa jam’iyyar ba za ta shiga cikin wata hadaka da kowace jam’iyya ba.
Sai dai a martanin da ya mayar, Atiku Abubakar ta hannun mataimakinsa kan yaɗa labarai Paul Ibe, ya jaddada bukatar fadada tattaunawa domin samun tattaunawa.