Kamfanonin samar da wutar lantarki sun yi barazanar dakatar da ayyukansu kan bashin Naira tiriliyan hudu da gwamnatin tarayya ke bin su.
A wata sanarwa da shugaban kwamitin amintattu na kamfanonin samar da wutar lantarki Col. Sani Bello mai ritaya ya fitar, ya ce ya zama dole su yi dauki wannan matakin sakamakon yadda bangaren samar da wutar lantarki ke fuskantar kalubale wajen cika alkawarin da suka dauka na inganta ayyukansu.
Sanarwar ta ce GenCos na ci gaba da shan wahala wajen samar da lantarki a Nijeriya amma tulin bashin da suke bin gwamnati, da matsalar kasuwar lantarki na ci gaba da kawo cikas ga shirin inganta bangaren lantarkin.