DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Wike ya ba mazauna Abuja shawarar yadda za su zauna lafiya da filayensu cikin tsari da doka

-

Ministan babban birnin tarayyar Nijeriya Abuja Nyesome Wike ya gabatar da sabuwar dokar filaye da za ta fara aiki daga ranar 21 ga Afrilu, 2025.
Dokar da ta haifar da muhawara mai zafi tsakanin masu ruwa da tsaki, inda ake ba da shawarwari kan matakan da mazauna Abuja za su dauka don kare kadarorinsu.
A cikin sanarwar da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar, an bayyana cewa dokar za ta taimaka wajen samun kudaden shiga ga hikumar babban birnin tarayya FCDA. Sai dai, wasu ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki sun nuna damuwa kan yadda dokar za ta shafi masu mallakar filaye a Abuja.
Gwamnatin tarayya ta yi kira ga mazauna FCT da su kasance masu lura da sabuwar dokar filaye, domin guje wa duk wata matsala da ka iya tasowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara