DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ba mu ciyo sabon bashi ba – Gwamnatin Katsina

-

 Ba mu ciyo sabon bashi ba – Gwamnatin Katsina 

Gwamnatin jihar Katsina ta musanta ikirarin da ofishin kula da basussuka, DMO, ya yi cewa gwamnatin jihar ta ciyo sabon bashi.

A wani rahoto da Ofishin kula da basussuka ya wallafa kwanan nan ya bayyana cewa jihar Katsina karkashin Gwamna Radda tare da wasu jihohin Nijeriya sun karbo sabon lamuni, domin cike gibi da aiwatar da wasu ayyuka da za su yi.

Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Dikko Radda, Ibrahim Kaula Mohammed, ya aike wa DCL Hausa, ta musanta rahoton wanda ta ke cewa a halin yanzu jihar ba ta ciyo wani sabon bashi ba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa babu wani sabon lamuni da gwamnatin Katsina a yanzu ta karba a karkashin Gwamna Radda amma wannan ba yana nufin gwamnatin jiha ba za ta ci bashi ba a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, za ta iya karbar bashi domin inganta rayuwar al’ummarta da ma jihar baki daya.

Sanarwar ta ce gwamnatin jihar na iya kokarinta wajen ganin ta bijiro da sabbin ayyuka da za su inganta rayuwar al’ummar jihar baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Barayin daji sun ba karnukansu jarirai ‘yan biyu da aka haifa a lokacin da suke tsare da mahaifiyarsu – Hon Sani Jaji

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kaura Namoda da Birnin Magaji a jihar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga da...

Akalla Mahajjatan Nijar 700 sun isa kasa mai tsarki

A ranar Talatar nan 13 ga watan Mayun 2025, rukuni biyu na farko na maniyyatan Nijar ya tashi zuwa kasa mai tsarki dauke da mutane...

Mafi Shahara