Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiSama da ma'aurata 10,000 ne suka yi tazarar haihuwa a jihohin Plateau...

Sama da ma’aurata 10,000 ne suka yi tazarar haihuwa a jihohin Plateau da Kebbi ta hanyar amfani da na’urar HUID

Wakilin kungiyar lafiya ta EngenderHealth a Nijeriya, Dr Kabiru Atta ya bayyana cewa an samu wannan nasara ne bayan wayar da kan jama’a na watanni 11, lamarin da ya sa ma’aurata suka karbi na’urar da hannu biyu.
Na’urar HUID dai tana bai wa ma’aurata damar yin tazarar haihuwa na tsawon shekaru 5.
A yayin wani taro, kwamishinan lafiya na jihar Kebbi, Yunusa Musa Ismail ya ce tsarin ya ceci rayuka da dama da kuma hana daukar cikin da ba a yi tsammani ba.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata