Rahotanni na nuni da cewa kalla mutane 23 sun halaka a wasu jerin hare-haren da aka kai a wasu kananan hukumomi hudu na jihar Benue.
Daily Trust ta ruwaito cewa kananan hukumomin da abin ya faru sun hada Guma, Logo, Ukum, da Kwande.
Mazauna yankin sun ce sabbin hare-haren da aka kai a baya-bayan nan sun tilasta wa da dama barin yankunansu.
Shaidun gani da ido sun ce an halaka mutane tara a karamar hukumar Logo, takwas a Ukum, yayin da kananan hukumomin Guma da Kwande aka halaka mutum uku, adadin da ya kai 23 da suka mutu.