DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Lakurawa sun yi ajalin mutane 13 a harin da suka kai garin Dede da ke karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi

-

Nasir Idris

A wani harin ramuwar gayya kan halaka shugaban Lakurawa Maigemu, da hadin gwiwar jami’an tsaro suka yi a ranar Alhamis din da ta gabata, a ranar Lahadin karshen mako kungiyar Lakurawa ta kai hari a yankin Birnin Dede da ke karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi da suka halaka mutane 13.

Google search engine

Kungiyar wadda ta kunshi mutane daga kabilu daban-daban da suka hada da Hausawa, Fulani, Toureg, Barebari da sauran kabilu, ta dade tana aikata ta’addanci a jihar Kebbi da kewaye.

Wani dan yankin jihar Kebbi, Musa Gado, ya ce ‘yan ta’addan sun kuma kona kauyuka takwas da ke yankin a yayin harin, da ya ce, maharan sun bar wani kauye daya kacal da sojoji ke gadi.

Wani dan yankin mai suna Suleiman Abubakar, wanda ya ce ya rasa dan uwan sa a harin, ya shaida wa Daily Trust cewa, ‘yan ta’addan sun mamaye al’ummar yankin ne da daddare, bayan kammala sallar magrib.

Sauran kauyukan da maharan suka kona sun hada da; Birni Garin Nagoro, Yar Goru, Dan Marke, da Tambo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan majalisar dokoki 6 a Jihar Zamfara sun fice daga PDP zuwa APC

‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara 6 da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC, suna zargin take...

Kotu ta umurci hukumar EFCC ta gabatar da kwamshinan kudi na jihar Bauchi ga kotu bisa zargin safarar N4.6bn

Kotun Tarayya da ke Abuja ta umurci Hukumar EFCC da ta gabatar da Kwamishinan Kuɗin Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, a ranar 30 ga Disamba domin...

Mafi Shahara