Kungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya ASUU ta zabi Farfesa Chris Piwuna, kwararren likitan kwakwalwa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos, a matsayin sabon shugabanta na kasa.
Farfesa Piwuna, wanda kuma shi ne shugaban sashen kula da harkokin dalibai sato Dean Student Affairs a Jami’ar Jos, ya karbi ragamar shugabancin daga hannun Farfesa Victor Osodeke, masani a fannin kimiyyar kasa daga Jami’ar Noma ta Michael Okpara da ke Umudike, Jihar Abia.
An yanke wannan hukunci ne a yayin babban taron zaben sabbin shugabannin kungiyar na kasa karo na 23, da aka gudanar a garin Benin na jihar Edo.