Hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON ta tabbatar da cewa jimillar mahajjata 7,263 daga kasar aka rigaya aka yi jigilarsu zuwa birnin Madina, na Saudiyya.
Rahoton PUNCH ta bayyana cewa aikin jigilar mahajjata na shekarar 2025 na kara samun tagomashi, inda aka samu jirage 18 zuwa Saudiyya daga Nijeriya tun bayan fara aikin a ranar 9 ga watan Mayu.
Yayin da aka fara aikin jigilar mahajjatan ke tafiya yadda ya dace a wasu jihohin, akwai wasu jihohin da har yanzu ba su fara jigilar mahajjata ba, ciki ha da wasu daga Arewa irin su Kano, Sokoto, Zamfara, Katsina da Borno.
Amma mahajjatan jihohin Bauchi, Kebbi, Osun, Oyo da Imo tuni suka fara isa Saudiyya.



