DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kamfanin Orano mai aikin hakar ma’adanan uranium ya shigar gwamnatin Nijar kara bisa kama wani babban jami’in kamfanin

-

Kamfanin Orano na kasar Faransa mai aikin hakar ma’adanan uranium a Nijar ya ce ya garzaya kotu domin domin kalubalantar kamun da gwamnatin Nijar ta yi wa wani babban jami’in kamfanin a ofishinsa da ke a birnin Yamai.

Kamfanin dai ya bayyana hakan ne a ranar 13 ga watan Mayun nan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shainsa na yanar gizo, inda ya ce wannan kamu ya saba doka.

A cewar kamfanin tun a ranar 5 ga watan Mayu ne wasu jami’an tsaro suka kutsa ofisoshin ma’aikatansa suka kwashe na’urorin komfutoci tare da kwace wayoyin ma’aikatan.

Kamfanin ya kara da cewa, a yayin wannan samame ne da jami’an tsaron suka yi awon gaba da babban daraktan kamfanin Orano Malan Ibrahim Courmo kuma har yanzu kamfanin bai samu damar yin magana da shi ba, tsawon kwanaki takwas kenan ake tsare da shi.

Kazalika kamfanin ya ce a yanzu haka jami’an tsaron sun yi wa ofishin kamfanin kawanya.

Tun bayan juyin mulkin Yulin 2023 dai ake ta kai ruwa rana tsakanin kamfanin Orano da hukumomin mulkin sojan Nijar.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu is a highly skilled and experienced broadcast journalist and fact-checker. Ukashatu has over five years of experience in writing, editing, and presenting news and program content for radio and television. As a dedicated and hardworking professional, He is committed to upholding the values of accuracy, fairness, balance, independence, and accountability in her reporting and programs.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kada mahajjaci ya rike kudin da suka wuce Riyal 60,000 a kasar Saudiyya – Jan hankalin NAHCON ga Alhazan Nijeriya

Hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON ta shawarci mahajjatan kasar da su guji daukar kudi sama da Riyal 60,000 na Saudiyya domin...

Mun yi kuskure a sakamakon da muka fitar na dalibai – Hukumar JAMB

Cikin alhini da nadamar abin da ya faru, hukumar JAMB da ke shirya jarabawar neman shiga makarantun gaba da sakandare a Nijeriya ta karbi duk...

Mafi Shahara