A ranar Talatar nan 13 ga watan Mayun 2025, rukuni biyu na farko na maniyyatan Nijar ya tashi zuwa kasa mai tsarki dauke da mutane akalla 700.
Ana kuma sa ran tashin jirgi na uku a wannan rana ta Laraba.
Sama da maniyyata dubu 12 ne ake sa ran za su gudanar aikin hajji daga Jamhuriyar Nijar, ciki kujera sama da dubu 15 da Saudiyyar ta ware wa kasar.
Da farko dai an tsara tashin jirgin farkon a ranar 8 ga watan Mayun nan to amma saboda wasu dalilai aka daga tafiyar zuwa Talata 13 ga watan Mayu.



