Tsohon shugaban kasa na mulkin soja a Nijeriya Janar Yakubu Gowon mai ritaya, ya bayyana cewa duk da cewar dimokuradiyya tana da kura-kurai, lokaci ya yi da mulkin soja zai zama tarihi a Nijeriya.
Janar Gowon ya bayyana hakan ne a Abuja yayin bikin kaddamar da wani littafi mai suna “Military Factor in Nigerian History, 1960-2018” da kungiyar masu nazarin tarihi ta Nijeriya HSN ta wallafa, a matsayin wani bangare na shagulgulan cika shekara 70 da kafuwar kungiyar.
Ya ce duk da cewa sojoji da gwamnatocin soja daban-daban sun ba da gudunmuwa wajen ganin an tabbatar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin Nijeriya, ya zama wajibi su ci gaba da goyon bayan ci gaban dimokuradiyya da cigaban kasa baki daya.



