Shekaru 15 cur kotun daukaka kara a Mauritaniya ta yanke wa tsohon shugaban kasar Mohamed Ould Abdel Aziz hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari, saboda amfani da ofishinsa ba bisa ka’ida ba da kuma tara dukiya ta haram.
Ould Abdel Aziz, wanda ya hau mulki ta hanyar juyin mulki a shekarar 2008, ya daukaka kara daga hukuncin farko na daurin shekaru biyar da aka yanke masa shekaru biyu da suka gabata bayan an same shi da laifin amfani da matsayinsa wajen tara dukiya.
Tsohon shugaban kasar, wanda ke tsare tun lokacin da shari’ar farko ta fara a watan Janairun 2023, ya bayyana tare da wasu tsofaffin manyan jami’an gwamnati da masu ba shi shawara, wadanda su ma ke fuskantar tuhume-tuhume na amfani da ofisoshinsu ba bisa ka’ida ba.
Kotun da ke babban birnin kasar, Nouakchott, ta kuma tabbatar da kwace dukiyar Aziz da kuma karbe masa ‘yancin zama dan kasa mai cikakken iko.
Aziz, mai shekaru 68, bai nuna wata alamar damuwa ba lokacin da aka sanar da hukuncin, a cewar kamfanin dillancin labaran AFP.
Masu bincike sun kiyasta cewa Aziz, wanda ya shugabanci kasar da ke yammacin Afrika mai mutane miliyan 4.5 na tsawon fiye da shekara goma, ya tara dukiya da kadarori da kudinsu ya kai dala miliyan 70 a lokacin mulkinsa.



