Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Dr. Agbo Gilbert Major, ya bayyana cewa Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya, ba halastaccen da jam’iyyar ne ba.
Yayin da yake magana a shirin Daily Politics na Trust TV, Gilbert ya ce jam’iyyarsu ba ta da wata alaka da Kwankwaso, yana mai cewa Kwankwaso ya bar jam’iyyar NNPP tun shekarar 2023 kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Yayin da yake tsokaci kan yawaitar sauya sheka da ‘yan manyan jam’iyyun adawa ke yi a kasar, ciki har da NNPP, Gilbert ya ce, “Kwankwaso ya zo da mutanensa, wato masu kiran kansu Kwankwasiyya. Idan ka duba tarihin mutanen da suka fice daga jam’iyyar, za ka ga cewa sun kasance cikakkun ‘yan tafiyar Kwankwasiyya. A gaskiya, su ne suka taka muhimmiyar rawa wajen nasarar NNPP a Kano.”
Sai dai ya kara da cewa wadanda suka bar jam’iyyar NNPP sun yi hakan ne saboda sun gaji da yadda tafiyar Kwankwasiyya ke gudana, amma ba su da wata matsala da jam’iyyar NNPP kanta.