DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jami’an tsaro sun kama wani mai garkuwa da mutane yana shirin tafiya aikin hajji a Abuja

-

Jami’an tsaro sun kama wani da ake nema ruwa a jallo bisa laifin garkuwa da mutane a sansanin aikin hajji da ke Abuja.

Wata majiya daga cikin jami’an tsaro da ke aiki a sansanin ta tabbatar wa da jaridar Daily Trust kama wanda ake zargin, a ranar Lahadi.

Majiyar ta ce an cafke wanda ake zargin ne yayin tantance mahajjatan da ke shirin tashi zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.

Majiyar ta bayyana cewa wanda ake zargin mai suna Yahaya Zango, mazaunin unguwar Paikon-Kore ne da ke karamar hukumar Gwagwalada a cikin babban birnin tarayya Abuja.

Jami’in tsaron ya ce hukumomin tsaro sun ayyana Yahaya a matsayin wanda ake nema, bisa zargin hannu da yake da shi a wasu laifukan garkuwa da mutane.

Ya kara da cewa wanda ake zargin ya gabatar da fasfonsa tare da sauran mahajjata daga Abuja da ke kan hanyarsu ta zuwa Saudiyya domin aikin hajji na bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan bindiga sun yi ajalin mutum 3 tare da sace 26 a Zamfara

Akalla mutane uku ne rayukansu suka salwanta aka kuma sace wasu 26 a wani sabon harin da ‘yan bindiga suka kai karamar hukumar Kauran Namoda...

Hadakar da nake sha’awa ita ce yaki da yunwa da Talauci a fadin Nijeriya

A yayin da ake ci gaba da rade-radin yiwuwar hadaka tsakanin jiga-jigan ‘yan adawa don tunkarar shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027, tsohon dan...

Mafi Shahara