Gwamnatin Jihar Katsina ta nemi a soke jarrabawar harshen Turanci da Hukumar WAEC ta gudanar kwanan nan, sakamakon jinkirin da aka samu a fara jarrabawar a fadin kasa.
Kwamishinar Ilimi na Firamare da Sakandare, Hajiya Zainab Musa-Musawa, ta bayyana matsayar gwamnatin ne yayin ziyararta ofishin WAEC da ke Katsina, inda ta ce an gabatar da koke a hukumance da sa hannun Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Hajiya Ummukhair Ahmed.
Rahoton kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya bayyana cewa WAEC ta danganta jinkirin da kokarin dakile satar amsa ne.
Musa-Musawa ta bukaci iyaye, makarantu da al’umma su kasance masu hakuri har sai an kammala bincike kan batun.



