DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan sanda sun kama mutumin da ake zargi da keta haddin ‘agolarsa’ a Bauchi

-

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi sun samu nasarar dakile wani yunkurin kai hari da matasa suka shirya yi wa wani mutum mai shekaru 37 da haihuwa da ake zargi da cin zarafin diyar matarsa wato ‘agolarsa’ mai shekaru 15.

A cewar rundunar, jami’an da ke karkashin shirin “Operation Restore Peace” wanda CSP Kim Abert ke jagoranta, sun samu bayanan sirri masu inganci wanda ya ba su damar dakile harin da ake shirin kai wa mutumin mai suna Wisdom Benoie.

Google search engine

Kakakin rundunar, SP Ahmed Wakil, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Bauchi.

Sanarwar ‘yan sandan ta ce binciken farko-farko sun bayyana cewa mutumin na auren mahaifiyar budurwar ne. Wanda ake zargin ya amsa laifinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsare-tsaren Tinubu na farfaɗo da martabar Nijeriya a duniya -Kashim Shatima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce gyare-gyaren da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa na sake gina martabar Nijeriya a idon duniya tare...

Gwamnatin Nijeriya na shirin dakatar da shigo da kayan tsaro daga waje

Gwamnatin Nijeriya ta yi niyyar kera dukkan makami da ake buƙata a cikin gida nan da shekara biyu zuwa biyar masu zuwa. Minista a ma'aikatar Tsaron...

Mafi Shahara