DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tarihin marigayi Aminu Dantata

-

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Najeriya ta yi babban rashi – na dattijo, attajiri, mai hangen nesa da zuciya mai tausayi: Alhaji Aminu Alhassan Dantata.
Ya rasu yana da shekaru 94 wato dai an haife shi a ranar 19 ga Mayu, 1931 a sanannen gidan attajirai na Alhassan Dantata da ke birnin Kano.

Tun lokacin da ya fara samun kudin kansa, Aminu Dantata, ya ci gaba da al’adun da dabiu irin na mahaifinsa – na daukar nauyin hajji ga Musulmi masu karamin karfi. Yana bayar da dabbobi a lokacin Babbar Sallah domin tallafa wa mabukata, kuma ya sanya duka zuriyarsa – har zuwa jikoki da su ci gaba da wannan aiki na alheri.
Bayanai daga shafin Wikipedia sun ce tun yana saurayi a 1948, ya shiga harkar kasuwanci a kamfanin mahaifinsa Alhassan Dantata & Sons a matsayin mai sayen amfanin gona. Daga nan ya tashi zuwa matsayin manaja na yankin Sakkwato a 1955, kafin ya zama mataimakin darakta a 1958. Bayan rasuwar yayansa Ahmadu a 1960, shi ne ya karbi ragamar shugabancin kamfanin.

Google search engine

A lokacin da Najeriya ta samu’yancin kai, Aminu Dantata ya riga ya zama daya daga cikin manyan ‘yan kasuwa. Ya kafa kamfaninsa na gine-gine wanda ya samu kwangilar gina wani bangare na makarantar koyon tukin jirgin sama ta Zariya a shekarar 1960.
Ya kasance memba a bankin bunkasa masana’antu na Najeriya a wancan lokacin wato (Nigerian Industrial Development Bank) daga 1964. A siyasance kuma, ya rike mukamin kwamishinan kasuwanci da tattalin arziki na Jihar Kano daga 1968 zuwa 1973 karkashin Gwamna Audu Bako.

Alhaji Aminu bai tsaya a kan kasuwanci kadai ba. Ya kasance daya daga cikin wadanda suka kafa Express Petroleum & Gas Company Ltd, kuma daga cikin wadanda suka bayar da gudunmawar kafa Jaiz Bank – bankin Musulunci na farko a Najeriya, kamar yadda shafin Wikipedia ya nunar.

Haka zalika, ya ba da gudunmuwa sosai wajen wajen kafa Kano State Foundation, gidauniyar da ke bayar da tallafin karatu da jari ga ‘yan kasuwa kanana.
Duk da dukiyar da daukakar da ya samu, Baba Aminu, kamar yadda mutane ke kiransa, ya fi son zaman lafiya da rayuwa mai natsuwa. A cewar Dr. Munzali Dantata cikin wata hira da jaridar Daily Trust, a kwanakin baya ya ce “Baba Aminu Dantata ya rungumi ilimi da jinkai. Ya sanya mu duka a makaranta tun muna yara, a makarantu mafiya inganci a kasar nan.”

Da fatan Allah Ya gafarta masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Jaridar Punch ta gano hakikanin abin da ya sa Ganduje ya ajiye mukamin shugabancin APC

Bayanai sun fara fita dalla-dalla kan dalilan da suka sa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya yi murabus daga mukaminsa a ranar Juma’a. Rahoton...

Babu wani jami’in gwamnatin jihar Plateau da ya zo yi mana ta’aziyyar mutanenmu da aka yi ajalinsu – Sarkin Zazzau

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Amb Ahmed Nuhu Bamalli, ya nuna damuwarsa kan yadda babu wata tawagar jami'an gwamnati daga Jihar Plateau da ta zo Zaria...

Mafi Shahara