DCL Hausa Radio
Kaitsaye

George Akume Har Yanzu Shi Ne Sakataren Gwamnatin Tarayya – Fadar Shugaban Kasa

-

Fadar Shugaban Nijeriya ta musanta jita-jitar da ke yawo cewa an sauke Sanata George Akume daga matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF).

A wata sanarwa da mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yada labarai da dabarun sadarwa, Mista Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Asabar, 28 ga Yuni, 2025, an bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da wannan ƙaryar da gwamnati ta ce “makircin masu yada jita-jita ce kawai.”

Google search engine

“Ba a sauya matsayin Mai Girma, Sanata George Akume, a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya ba,” in ji Onanuga.

Ya ƙara da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ke kan ziyarar aiki a ƙasar Saint Lucia, bai nada kowa sabon mukami ba.

Wannan bayani ya zo ne a daidai lokacin da jita-jita ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an cire Akume daga kujerarsa, inda wasu ke cewa an maye gurbinsa da Hadiza Bala Usman.

Fadar Shugaban Nijeriya ta ce tana fatan wannan ƙarin haske zai dakile yaɗuwar labaran ƙarya da ke barazana ga kwanciyar hankali.

Sanata George Akume, tsohon gwamna kuma gogaggen ɗan siyasa, ya hau kujerar Sakataren Gwamnatin Tarayya tun a watan Yuni 2023, kuma har yanzu yana daga cikin manyan jiga-jigan gwamnatin Shugaba Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Nijeriya na iya shiga karin yanayin matsalar tsaro sakamakon karuwar yawan jama’a – Bankin Duniya

Shugaban Bankin Duniya, Ajay Banga, ya gargadi Nijeriya da sauran kasashen duniya cewa idan ba a dauki matakan gaggawa da hadin gwiwa ba, karuwar yawan...

APC ba ta da juriyar ra’ayoyin jam’iyyun adawa – Rauf Aregbesola

Sakataren jam’iyyar ADC Ogbeni Rauf Aregbesola, ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da rashin jurewa ra’ayoyin 'yan adawa da kuma amfani da ƙarfin gwamnati wajen...

Mafi Shahara