Kungiyar dattawan Arewa ta bayyana yadda ‘yan bindiga suka kashe sojoji kusan 20 a matsayin fito-na-fito da gwamnatin Nijeriya, kuma alama ce ta tabarbarewar tsaro a Arewacin kasar.
Mai magana da yawun kungiyar, Farfesa Abubakar Jiddere ya bayyana cewa kungiyar ta yi tir da harin da aka kai ma sojojin kuma hakan na nuna irin yadda rashin tsaro ya dabaibaye yankin.
Kungiyar ta gargadi gwamnati kan rashin daukar mataki ya fara sa ‘yan kasa sanya alamun tambaya ga gwamnati game da iya kare rayukansu.
‘Yan bindigar dai sun yi ma sojojin kwantar-bauna a Mariga a cikin farkon wannan satin inda sojoji 20 suka rasa rayukansu.