Hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON ta fitar da cikakken jadawalin shirye-shiryen aikin Hajjin 2026/1447H, wanda aka tsara a matakai bakwai daga watan Yuni 2025 zuwa Afrilu 2026.
Mataki na 1 – Shirye-shirye (Yuni 2025)
An fara jadawalin ne a ranar 8 Yuni 2025 (12 Dhul-Hijjah 1446H) da karɓar takardun shiri da jadawalin aiki daga Saudiya, tare da fitar da jagororin wayar da kai ga maniyyata da hukumomi.
Mataki na 2 – Fara yarjejeniyoyi na Mashair (a tsakanin 6-24 na Satumba), za kuma a fara tura kudi zuwa e-wallet na shafin NUSUK.
Mataki na 3 – Rijista da rarraba aikace-aikacen bangarori (Oktoba 2025)
Za a rufe rijistar maniyyata a ranar 12 Oktoba 2025 (20 Rabi’ al-Thani 1447H). Dukkan jihohi da hukumomi za su shigar da bayanan maniyyata da rarraba su cikin bangarori ta hanyar tsarin Nusuk.
Mataki na 4 – Kammala ba da kwangiloli (Nuwamba 2025 – Janairu 2026)
Za a rattaba hannu kan yarjejeniyar tafiya da cika takardu daga 8 Nuwamba 2025 zuwa 4 Janairu 2026, ciki har da biyan kuɗin sansanoni da tabbatar da jadawalin jiragen sama.
Mataki na 5 – Masauki (Janairu – Fabrairu 2026)
Za a kammala shirye-shiryen masauki a Makkah da Madinah zuwa 1 Fabrairu 2026, yayin da za a kammala shigar da kwangilolin masauki a tsarin Nusuk kafin 6 Fabrairu 2026.
Mataki na 6 – Visa (Fabrairu – Maris 2026)
Fitar da bizar Hajji za ta fara a ranar 25 Fabrairu 2026 (1 Shawwal 1447H) kuma za ta ƙare a 20 Maris 2026 (12 Shawwal 1447H).
Mataki na 7 – Kammalallen shiri (Maris – Afrilu 2026)
Za a fara loda bayanan zuwan maniyyata daga 25 Maris 2026, a mika ragamar sansanoni zuwa hukumomi a 15 Afrilu 2026, sannan maniyyata za su fara isa a ƙasar Saudiyya daga ranar 16 Afrilu 2026.
Wannan jadawali ya yi daidai da na Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya, kuma an tsara shi ne domin tabbatar da tsari da sauƙin tafiyar aikin hajji ga ’yan Najeriya kamar yadda hukumar NAHCON ta fitar.