Rundunar ‘yan sandan Jihar Yobe ta tabbatar da cewa wani Hamisu Ali mai kimanin shekaru 55 ya yi ajalin matarsa mai shekaru 40 a garin Babangida da ke a karamar hukumar Tarmuwa ta Jihar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar, Dungus Abdulkarim ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar safiyar Juma’a.
Ya kuma kara da cewa, a ranar 28 ga Yuni ne suka amsa kira daga mazauna kauyen Koriyel inda suka shaida musu cewa Hamidu ya sassari matarshi inda ya yi sanadiyar ajalinta kuma ya gudu. Amma Rundunar na bakin kokari wajen ganin ya shiga hannu.