Daga watan Maris 2024 zuwa Mayun 2025, gwamnatin tarayya ta raba Naira tiriliyan 1.6 ga jihohi 36 da babban birnin tarayya (FCT) domin ayyukan more rayuwa da tsaro.
Wannan na kunshe ne a cikin wani rahoto daga Ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF), da aka mika wa kwamitin rabon kudin tarayya a watan Mayun 2025 don inganta tsaro da habbaka ilimi da lafiya a jihohin.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an fito da kudin ne daga ajiyar kudaden shiga da ba na bangaren mai ba, karkashin shirin tallafin gaggawa da aka kafa bayan cire tallafin man fetur.
An fara rabon da N200bn a Maris 2024, yayin da aka ci gaba da raba kusan N100bn a kowane wata. Babban adadin da aka raba a wata guda shi ne N222bn a watan Mayun 2024.
Duk da wannan yawan kudi, rahoton bai fayyace yadda kowace jiha ta karɓi nata rabon ba. Sai dai Naira N1.7, da asusun ya tara an yi amfani da N1.6tn, ya rage N100bn a asusun.