Peter Obi da ya yi wa jam’iyyar LP takarar shugaban kasa a zaben 2023 ya bayyana cewa zai sake tsayawa takarar kujerar Shugaban Ƙasa a shekarar 2027.
Tsohon Gwamnan jihar Anambra ya kuma yi watsi da jita-jitar cewa zai tsaya takarar mataimakin Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP a yayin zaben.
A cikin shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels Peter Obi ya zai tsaya takarar ne don ya cancanta.
Da aka tambaye shi ko yana shirin zama mataimakin Atiku a zaɓen 2027, Obi ya ce, “wannan maganar babu ita; babu wanda ya taɓa tattaunawa da ni a kai. Mutane na ɗaukar abubuwa da yawa da kansu. Babu wanda ya taɓa zama da ni.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya jaddada cewa har yanzu mamba ne mai ƙwazo a jam’iyyar Labour Party, kodayake yana cikin gamayyar jam’iyyun adawa ƙarƙashin African Democratic Congress (ADC), da aka kafa don ƙwace mulki daga hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ke neman wa’adin mulki na biyu a shekarar 2027.



