DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Rundunar sojin Nijeriya ta ce sojoji sunyi ajalin ‘yan ta’adda 358 tare da kama 431 a cikin watan Janairun 2025

-

CDS Christopher Musa

Google search engine

Daraktan yada labarai na rundunar Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, inda ya ce rundunar na ci gaba kai hare hare ga ‘yan ta’adda da masu tada kayar baya a fadin kasar.

A cewar sanarwar sojojin sun kama mutane 59 da suka aikata laifin satar mai tare da ceto mutane 249 da aka yi garkuwa da su.

Sanarwar ta kuma kara da cewa sojojin sun kwato makamai 370 da alburusai 4,972 da suka hada da bindigogi kirar AK47 guda 105, bindigogi kirar gida guda 25, da karin wasu bindigogin guda 32, da kuma albarusai 3,066.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin tabbatar da inshorar lafiya a dukkanin hukumomi da ma’aikatun gwamnatin Nijeriya

Shugaba Bola Tinubu ya umarci sakataren gwamnatin tarayya da ya fitar da takardar umarni ga dukkan ma’aikatu da hukumomi domin tabbatar da inshorar lafiya bisa...

Zan iya kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga cikin watanni biyu muddin na samu iko da hukumomin tsaro – Gwamnan Zamfara

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa matsalar ayyukan ’yan bindiga da ke addabar jihar za ta zama tarihi muddin ya samu damar bayar da...

Mafi Shahara